<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>452</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ku tashi dai mutane
 Ku bi Ubangiji
 Ku tada tutar nasa
 Tuta na shaidarsa
 Zai ba mu nasara kuwa
 Bisa magabcin mu
 Har dukan mutanenmu
 Su san Mai Cetonmu.

[V2]
 2) Ku tashi dai mutane
 Ku yi biyayya kuwa
 Ku shiga yaƙin Kristi
 Ku bi Maganarsa
 Kada ku koma baya
 Amma ku ƙarfaffa
 Don duniya za ta shuɗe
 Duk da kwaɗayinta.

[V3]
 3) Ku tashi dai mutane
 Ku shaida Bishara
 Ta wurin ikon Yesu
 Ku nuna ƙamnarsa
 Ku yafa sulken kirki
 Ku yi addu'a kuwa.
 Har ran da Yesu Kristi
 Zai ka mu gidansa.</lyrics>
<title>Ku Tashi Dai Mutane, Ku Bi Ubangiji LW452</title>
<author>C. Barny Robertson, George Duffield, George J. Webb</author>
</song>